Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta harba makamai masu linzami fiye da 40 a Haifa a 'yan mintoci da suka gabata, wasu daga cikinsu masu nauyi ne. A sa'i daya kuma, Iran ta harba makamai masu linzami a yankunan da aka mamaye kuma an ji kararsu a duk fadin Isra'ila.

A gefe guda kuma Hizbullah ta fitar da sanarwar gargadi ga mazauna garuruwan Kariat Shamuna da Nahharia da ke arewacin yankunan da aka mamaye da su bar wadannan yankuna da wuri-wuri su tafi kudu tun kafin Hare-Hare su shafe su.
Your Comment